Za a kai gwamnatin Amurka kara saboda shafin facebook na karya

Hakkin mallakar hoto AP

Wata mata zata kai karar gwamnatin Amurka bayan da gwamnatin ta kirkiri wani shafin facebook dauke da hotunan matar wanda kuma ke nuna tsiraicinta

Ma'aikatar shari'ah ta Amurkar ta amince cewa daya daga cikin masu yiwa ma'aikatar aiki ne ya kirkiri shafin ba tare da ya fadawa Sondra Arquiett ba.

Amma sai dai ma'aikatar ta ce tunda farko Ms Arquiett ta amince a yi hakan saboda ta baiwa jami'an ma'aikatar damar shiga wayar salularta

Ana sa ran fara shari'ar a mako mai zuwa a New York tare da gwamnatin Amurka da kuma wani ma'aikacin hukumar yaki da miyagun kwayoyi Timothy Sinnigen

Wannan al'amari dai ya kai shekaru 4 yanzu haka amma kafar watsa labarai ta Buzzfeed te ta fara bada rahoto a kai

Hotunan kananan yara

An kirkiri shafin facebook din na karya bayanda aka tsare Ms Arquiett ma'aikaciyar wani gidan cin abinci a watan Yulin shekarar 2010 sannan aka zarge ta da hannu a harkar miyagun kwayoyi

A lokacin da aka tsare ta, Ms Arquiett ta mika wayar salularta da kuma amincewa jami'ai su duba bayanan dake cikin wayar domin taimaka musu wajen gudanar da bincikensu

Wannan ya hada da bincike akan saurayinta Jermaine Branford wanda ake zargin yana tsara harkar sayar da kwayoyi

Sai dai Ms Arquiett ta ce ba a fada mata cewa wannan aikin zai hada da kirkirar wani shafin facebook ba, da wani sunan da aka san tana amfani da shi na Sondra Prince

Hakkin mallakar hoto AP

Shafin ya kuma kunshi hotunanta da kuma na danta da kuma wata 'yaruwarta

Daya daga cikin hoton na nuna tsiraicinta in ji lawyanta

Ms Arquiett ta ce wannan ya ci karo da 'yancin da take da shi na sirrinta da kuma kariya karkashin doka da kuma bin ka'ida don haka ne ta bukaci a biya ta $250,000 domin bata masa suna

Kamfanin dillacin labarai na AP wanda ya dauki hoton shafin ya nuna cewa shafin na karya na da abokanai 11 kafin a cire shi

Gwamnatin Amurka dai ta amince da cewa Mr Sinnigen ya kirkiri shafin kuma ya yi amfani da shi wajen tura bukatar neman abokantaka ga wani wanda ake nema da kuma amincewa da kulla abokantaka da wasu, amma sai dai gwamnatin ta musanta cewa ta bayyana shafin a bainar jama'a

Sai dai kafar yada labarai ta Buzzfeed da kuma kamfanin dillacin labarai na AP dukkaninsu sun iya shiga shafin kafin a cire shi daga internet