CAR: Sabon rikici ya sake barkewa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane fiye da 5,000 ne suka mutu tun lokacin da rikicin bangarancin ya barke a karshen 2013

An sami barkewar wani sabon tashin hankalin a babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na Bangui.

Shi ne tashin hankali mafi muni da aka gani tun lokacin da Majalisar dinkin duniya ta karbi aikin samar da zaman lafiya a garin a watan daya gabata.

An kashe akalla mutane biyar a yini daya. kuma Wani sojin kiyaye zaman lafiya na MDD ya mutu a wani hari daga bisani.

Wakilin BBC a Bangui yace ansa dokar takaita zirga zirga a garin. An kuma lalata gidaje da kuma lalata harkokin kasuwanci da banka musu wuta. Sojojin Kiyaye zaman lafiyar dai sunyi ta kokarin su dakatar da fadan tsakanin musulmi da Kirista, wanda aka soma a ranar Talata.