Ebola: Nigeria za ta aika jami'an sa-kai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya yi shelar warkewar mutum na karshe da ya yi fama da Ebola

Gwamnatin Nigeria ta ce za ta aika gudunmawar jami'an lafiyan sa-kai zuwa kasashen Afirka ta yamma masu fama da cutar Ebola a kokarin shawo kan cutar.

Karamin Ministan lafiya na Nigeria, Dr. Khaliru Alhassan ne ya bayyana haka a wani taron kwararru don binciken hanyoyin tunkarar Ebola da ma sauran cutuka da ka iya barkewa a kasar.

Ya ce ana ci gaba da yi wa jami'an lafiyan rijista wadanda ya zuwa yanzu sun kai 200, kuma cibiyoyin lafiya na duniya sun taimaka wajen horas da su.

Gwamnatin Nigeria dai ta yi shelar samun nasara wajen shawo kan cutar Ebola a fadin kasar, tun bayan barkewarta sakamakon zuwan wani dan Liberiya da ke dauke da cutar.