Za a hana wasu jarumai bayyana a talbijin

Hakkin mallakar hoto CNS
Image caption An kama jaruman fina-finai da dama a China kan aikata miyagun lafiuka da ba za su kasance abin koyi ba

Hukumar kula da kafofin yada labarai a China ta ce za ta haramta wa jaruman fina-finan da aka samu da miyagun dabi'u bayyana a tashoshin talbijin din kasar.

Hukumar ta ce babu wani abin misali a dabi'un da wasu jaruman fina-finai ke nunawa a baya-bayan nan musammam ga matasa a kasar.

Rahotanni sun ce an kama wasu jaruman fina-finai a China da miyagun kwayoyi a bana, ciki har da dan shahararren jarumin fim din nan, Jackie Chan, wanda aka tsare bayan samun miyagun kwayoyi a gidansa.

An kuma tsare wani fitaccen mai shirya fina-finai sakamakon hulda da mata masu-zaman-kansu a kasar, wanda har lambar yabo ya taba samu.

A farkon wannan shekarar ma, mahukunta a China sun nemi 'yan sanda su dauki tsauraran matakai a kan masu harkar miyagun kwayoyi da caca da kuma hulda da mata masu-zaman-kansu.