Ana cigaba da fada kan garin Kobani

Yan gudun hijira da suka fito daga Kobani Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yan gudun hijira da suka fito daga Kobani

Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon tace tana iyakacin kokarinta wajen hana Dakarun mayakan Islama kwace garin Kobane na Syria.

Amma sai dai wani babban jami'i a ma'aikatar yace mayakan sun jima suna koyan dabarun kaucewa hare- haren da za'a iya kai musu ta sama.

Rundunar sojin Amurkar dai tace tayi imanin cewa mayakan kurdawa har yanzu suke da iko da garin, duk da irin hare- haren da aka kai musu a ranar Laraba

Wani shugaban mayakan kurdawa ya shaidawa kamfanin dilancin labaru na reuters cewa mayakn ISIS sun riga shigo cikin wasu sassa na gari yayinda ake cigaba a gwabza kazamin fada.

Sai dai idan mayakan ISIS suka yi nasarar kwace garin na Kobani to iyakar Syria da Turkiya zata kasance karkshin ikonsu.