'Ba a san halinda Shugaba Jong-un yake ciki ba'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An jima ba a ga Kim Jung un a bainar jama'a ba

Jam'iyya mai mulki a Korea ta Arewa na bukukuwan cika shekaru 69 cikin wani yanayi na rade- radin halinda Shugaban Kasar yake ciki.

Fiye da wata guda ke nan rabon da a ga Kim- Jong- Un a bainar jama'a, ana kuma tababar koma zai kasance a bukukuwan da za'a yi.

Bayanin da Kafar Yada labaran Kasar tayi game da lokacin da aka dauka mai tsaho babu duriyarsa shine na danganta shi da cewar yana fama da abinda ta kira 'rashin jin- dadi' abinda yasa ake ta rade- radin cewa bashi da lafiya sosai ,ko kuma wata gwagwarmaya ta iko na gudana a tsakanin manyan 'ya'yan jam'iyyar