Twitter: Vivian Schiller ta sauka daga mukaminta

Hakkin mallakar hoto
Image caption Twitter na daya daga cikin manyan shafukan sada zumunta a duniya

Wata babbar ma'aikaciya dake shugabantar bangaren labarai a Kamfanin Twitter ta sanar da cewa zata sauka daga kan mukaminta.

Vivian Schiller zata sauka ne bayan ta shafe kasa da shekara guda a kan aikinta

Yayinda take rubutu a shafinta na Twitter, Ms Schiller ta ce zata bar aikin ne don sabuwar shugabar Kamfanin Katie Stanton ta iya sake tsara abubuwa

An samu canje canje da dama game da yadda ake gudanar da kamfanin Twitter a bana.

Wasu tsoffin jami'an Twitter biyu da suka hada da shugaban sashen waka sun bar aikinsu a kwanan nan.

Hakkin mallakar hoto Getty

Sabon babban jami'in kamfanin Twitter ne ya bada sanarwar barin jami'ar aiki a shafin na sada zumunta a ranar Laraba.

Adam Sharp wanda ya soma aiki da Twitter a shekarar 2010 shi ne zai maye gurbin Ms Schiller.

A sanarwar data rubuta a shafinta na Twitter, Ms Schiller ta godewa tsohon babban jami'in ayyuka na Twitter Ali Rowghani da kuma Chloe Sladden wadanda suka mika takardunsu na barin aiki a rana guda a watan Yuni.

Ta ce tsofaffin abokanan aikinnata biyu ne suka karfafa mata gwiwar aiki a kamfanin na San Francisco.

Ta ce taji dadin aikin kamar yadda ta rubuta a shafinta na Twitter.

Ms Schiller ta taba yin aiki a CNN sannan ta yi wa jaridar New York Times aiki kamar yadda bayanan ayyukan da ta yi ya nuna.