WHO ta ce cutar Ebola ka iya karuwa

Yaki da cutar Ebola Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaki da cutar Ebola

Kungiyar lafiya ta duniya ta ce akwai yiwuwar karuwar masu dauke da cutar Ebola, muddin ba a samu karin taimako daga kasashen duniya ba.

Wani kakakin kungiyar ta WHO ya ce akwai kusan kashi daya bisa 3 na gadajen da ake bukata ga majinyata a kasashen da cutar tafi shafa.

Da ma dai Kungiyar Likitocin sa kai ta Medecins Sans Frontieres MSF ta ce an samu karuwar masu dauke da kwayar cutar Ebola matuka a Conakry babban birnin Kasar Guinea.

Kungiyar ta MSF ta kuma ce ta kasa gane shin me yasa wata guda bayan fara barkewar annobar,ba a aike da taimakon kayan aiki da ma'aikana kiwon lafiya ba.

Mataimakin shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO dai ya ce a yanzu cutar na kara yawa ne a manyan biranen kasashen da cutar tafi muni guda uku wato Liberia, Guinea da Saliyo.