Yan sandan sun bankado makamai a Anambra

Jamian yan sanda a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamian yan sanda a Najeriya

Yan sanda a Najeriya sun ce sun bankado miyagun makamai a wani gida a garin Nnewi a jihar Anambra.

Sun ce suna kokarin lalubo wasu mutane da take zargin sun boye miyagun makaman a wani kauye dake garin Nnewi.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Anambra ya bayanawa BBC cewa an gano harsasai sama da dubu daya da kuma bindigogi.

Bazuwar kananan miyagun makamai a hannun jama'a ba bisa izini ba dai, wata matsala ce dake cigaba da zama babban kalubale a Najeriya.