'Indiya za ta gawurta a fagen kwallon kafa'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Indiya ce kasa ta 158 a duniya amma masu shirya gasar sun ce za ta taimaka wajen zama hamshakiya ta fuskar kwallo a nan gaba duniya.

Tsohon kocin Sunderland da Manchester City Peter Reid ya ce sabuwar gasar Super League ta Indiya ka iya zama wani mafarin ci gaba na harkokin kwallon kafa a kasar.

Reid shi ne kocin kungiyar Mumbai City da ke fafatawa a gasar wadda kuma za ta bude karawarta a gidan Atletico De Kolkata ranar lahadi, ko da yake tikitin wasan 20,000 kacal aka saya a cikin dubu 68,000.

Ya ce kwallon kafa ta shiga Indiya, kuma abu daya da ya sani shi ne kwallon kafa za ta bunkasa, ya ce gasar tana da tsari da burgewa matuka.

Baya ga Reid akwai manyan gwarzaye a harkar kwallon kafa da ke bugawa a gasar da suka hadar da Alessandro Del Piero da Freddie Ljungberg da Robert Pires da David James.

Akwai kuma Nicolas Anelka da Marco Materazzi da Michael Chopra, yayin da gwarzon dan wasan Brazil Zico ke horas da kungiyar FC Goa.

Gasar za ta kasance ta makwanni 10, yayin da kungiyoyin kwallon kafa takwas za su fafata da nufin daukaka martabar kwallon kafa a wannan kasa da wasan kurket ta mamaye.