Ebola: Morocco ta nemi a daga gasar kwallon kafa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane kusan 4,000 sun mutu a Yammacin Afirka

Kafar yada labarai a Morocco ta ce gwamnati ta nemi a dage gasar cin kofin nahiyar Afirka da za'a yi shekara mai zuwa saboda barkewar cutar Ebola.

Wannan ya biyo bayan shawarar da ma'aikatar lafiyar kasar ta bayar na a kaucewa gudanar da dukkanin tarukan da zasu hada da kasashen da cutar ta bulla

An fahimci cewa jami'an kasar Moroccon zasu tattauna wanan bukata tasu a hukumance, tare da masu shirya gasar wato CAF, a mako mai zuwa.

Tuni dai aka dage wasannin neman cancantar shiga gasar da suka hada da kasashen da suke fama da cutar wato Gini da Liberia, da kuma wasan da za'a buga a Morocon ranar asabar