An bukaci Turkiyya ta bari a kare garin Kobane

Mayakan Kurdawa a Kobane Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan Kurdawa a Kobane

Jakadan majalisar dinkin duniya na musamman a syria ya bukaci kasar Turkiya ta kyale masu bada agaji su tsallaka zuwa Syria don kare garin Kobane, wanda ke fuskantar harin 'yan kungiyar ISIS.

Mr Staffan de Mistura wanda ya ambato wani sashe na majalisar dinkin duniya dake cewa, kowa na iya yin abinda ya ga zai iya don dakatar da kisan kiyashi.

Ya kuma ce har yanzu akwai akalla kusan mutane dari bakwai mafi yawansu tsofaffi wadanda ke garin Kurdawa da kuma wasu dubanni dake kan iyakar Turkiya da Syria.

Ya ce majalisar dinkin duniya bata bukatar sake ganin abin da ya faru a Bosnia cikin shekarar 1995 inda sojojin Serbiya suka hallaka musulmi maza da kananan yara.