Boko Haram sun sako wasu 'yan Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Jamhuriyar Kamaru Paul Biya ya ce an sako wasu mutane 27 da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka sace su.

Mutanen da aka sakon sun hada harda matar mataimakin fira-ministan kasar Ahmadou Ali wadda aka sace a watan Yuli da kuma wasu 'yan China goma da aka sace a watan Mayu, a kusa da iyakar kasar da Najeriya.

Babu tabbacin ko an biya kudin fansa kafin a sako mutanen.

Kungiyar Boko Haram ta fadada hare-harenta a 'yan kwanakin nan zuwa wasu yankunan arewacin Kamarun.

Rahotanni sun nuna cewa tuni har an dauki mutanen a jirgin sama an kai su Yaounde, babban birnin kasar.

Alhaji Shu'aibu Garkuwa, Garkuwan Ngoundere, da ke arewacin kasar, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa jama'ar Kamaru na farin ciki sosai akan sako mutanen.

Karin bayani