'Mazauna garin Kobane na mawuyacin hali'

Kobane Crisis Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Rikicin Syria

Wani babban jami'ain Kurdawa a garin Kobane ya shaidawa BBC cewa mayakan IS sun yi kokarin kai hari akan iyakar Turkiyya da Syria ba tare da da nasara ba.

Khalid Berkel yace mayakan sun kuma kai hari akan garin Kobane.

Dubban fararen hula ne suka makale a garin.

Babban jami'in Mr Khalid ya ce masu tayar da kayar bayan sun kaiwa birnin hari ne ta bangarori daban daban domin su ga sun kwace iko da shi.

Mayakan sa kai na Kurdawa da kuma yan tawayen sa kai na Syria sun ce suna bukatar karin makamai domin yakar yan kungiyar ta IS.

Wani babban jami'i a cikin dakarun Kurdawa Ismet Sheikh Hassan ya yi gargadin cewa za a iya samu matsalar kisan kiyashi idan har kungiyar IS ta kwace ikon garin na Kobane, a saboda haka ya bukaci taimako daga sauran kasashen duniya.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba