Faransa ta kama 'yan Alka'ida a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumomin Faransa sun ce sojojinsu da ke aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Sahel sun kai hari akan wani ayarin motocin 'yan Alka'ida masu dauke makamai.

Sojojin sun ce sun kuma yi nasarar kama wasu daga cikin mutanen.

Faransa ta ce mutanen sun fito ne daga kasar Libiya zuwa kasar Mali, kafun suyi kicibis da dakarun ta a hamadar arewacin Nijar.

Yankin Sahel din dai na fama da rikici daga masu tada kayar baya.