An sanya hotunan batsa a Snapchat

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kutse a Snapchat na shafar mutane miliyan 4.6 da ke amfani da shi

Masu kutse a intanet sun sanya hotunan batsa a Snapchat, tare kuma da barazanar kara sanya wasu. An rika tare hotunan da masu amfani da hanyar aika sakwannin ta Snapchat ta wasu hanyoyin (app)ba ta ainaahin hanyarsa suke aikawa.

Ana fargabar yawancin hotunan na yara ne kanana kasancewar galibi masu amfani da Snapchat din yara ne 'yan tsakanin shekaru 13 zuwa 17.

Sai dai kuma kamfanin shafin na Snapchat ya ce babu wani kutse da aka yi masa.

Ya kara da cewa, an zambaci masu aikewa da karbar sakonni ne wato masu amfani da shafin nasa ne da suke bi ta wasu hanyoyin ba ta ainahin hanyar shigar sa ba.

Ya ce daman kuma wannan abu ne da kamfanin ya hana a bisa sharadin amfani da Snapchat saboda daman ya sabawa tsarin tsaron masu amfani da shafin.

Image caption Ana iya ganin hotuna har da na bidiyo a Snapchat na dan lokaci kamar dakika biyar

Kamfanin ya ce yana sanya ido sosai a App Store da Google Play domin gano masu shiga shafin ta wasu hanyoyin da ba na ka'ida ba.

Kuma ya ce yana samun nasarar fitar da hotunan batsar da yawa.

Sai dai kuma masu bincike kan harkokin tsaron intanet sun ce dole ne kamfanin ya dauki alhakin wannan kutse.

Mark James kwararre kan tsaro na kamfanin tsaro na intanet na Slovania ESET, ya ce tun da dai Snapchat yana nuna ba a masa kutse, to akwai bukatar su tabbatar da sun hana masu yi musu kutse. Sai dai kuma wasu na tantamar sahihancin hotunan da msu kutsen ke sawa, da cewa na bogi ne.