Wata 'yar Amurka ta kamu da Ebola

Hakkin mallakar hoto

Wata jami'ar kiwon lafiya da ta yi jinyar wani mai cutar Ebola a Amuraka ta harbu da cutar.

Hukumomin kiwon lafiya a Jihar Texas sun ce sun gano hakan ne bayan sun gwada jinin matar a yammacin jiya asabar.

Sai dai sun ce za su yi wasu karin gwaje-gwaje akan matar wadda ba a bayyana sunanta ba.

Mutumin da ta yi jinyar sa din ya je Amurka ne daga Liberia.

Shine mutum na farko da ya kamu da cutar a Amurka.