Jami'an tsaro sun kai samame a Abuja

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya an kashe akalla mutane ukku a wani samame da ake zargin cewa sojoji sun kai a wajen garin Abuja.

An kai samamen ne a wurin da mutanen da suka tsere daga yankunan da ake rikici a kasar ke zaman gudun hijira.

An kuma jima wasu raunuka, aka kuma kama wasu da dama a samamen, wanda aka kai tsakar daren Asabar.

Wani dalibi mai zaman gudun hijira a wurin ya ce sojoji ne su ka je cikin dare suka harbe kimanin mutane ukku, suka kama wasu da dama.

Ya ce babu wanda ya yi masu bayanin dalilin kai samamen.

Ya ce wadanda ke zaune wurin da aka kai samamen mutane ne da suka gudo daga yankin arewa-maso-gabas, inda 'yan Boko Haram ke tada kayar baya, da ma wasu jihohin da ke fama da rikici.

Jami'an tsaro dai ba su ce komai ba akan lamarin.