Sojoji sun kai samame a Abuja

Sojojin Njeriya a bakin aiki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Najeriya dai na kai irin wannan samame ne domin tabbatar da doka da oda a kasar.

Akalla mutane uku aka hallaka a wani samame da ake zargin cewa sojoji sun kai a wata unguwa da ke Abuja babban birnin Najeriya.

Galibi mutanen da suka tsere daga yankunan da ake rikici a kasar ke zaman gudun hijira a wani wuri da ke unguwar Durumi a Abujar.

Rahotanni sun ce wasu sun samu raunuka yayin da kuma jami'an tsaron sun kama wasu da dama a samamen, wanda aka kai tsakar daren ranar Asabar.

Ko a watan satumbar shekarar 2013, jami'an tsaro da suka hada da sojoji da na jami'n tsaron farin kaya sun kashe mutane 8 a irin wannan sumame da suka kai a wani makeken gida da ke Unguwar Apo.

Inda suke zargin cewa akwai 'yan kungiyar Boko Haram a wurin, amma daga bisani bayan wani bincike da hukumar kare hakkin bil'adama ta gudanar ta zargi hukumomin tsaro da laifi kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.

saboda a cewar hukumar galibi wadanda aka kashe masu hayar Keke Napep ne har ma hukumar kare hakkin bil'adaman ta bukaci hukumomin tsaron da su biya iyalan wadanda aka kashe diyya.