'Yan Birtania na neman Google ya goge bayanansu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Facebook da Youtube na daga kamfanonin da dokar ta fi shafa a Turai

Dubban 'yan Birtania sun nemi kamfanin Google ya goge hanyoyin samun wasu bayanai da suka shafe su wadanda ba sa so jama'a su ci gaba da gani.

Wannan bukata dai tana karkashin dokar Turai ce da ake kira, ''right to be forgotten''.

Google ya ce ya fitar da hanyoyin samun bayanai har 498,737 tun daga watan Mayu na shekaran nan ta 2014.

Kuma wadannan sun hada da shafuka 63,616 sakamakon bukatun da aka gabatar masa daga Birtania.

Kamfanin ya ce bukata 18,304 aka gabatar masa daga Birtania, da wannan ita ce mafi girma ta uku a Tarayyar Turai.

Bukatar ta biyo bayan hukuncin da kotun Tarayyar Turai ta yi ne na fitar da duk wasu tsoffin bayanai ko marassa amfani idan aka bukaci hakan daga rumbun bayanai na Google.

Hukuncin ya haifar da kace-nace kan dokar tace wa ko takunkumi akan bayanai.

Hakkin mallakar hoto AFP

Google ya bayyana cewa ya fitar da kashi 35 cikin dari ko 18,459 na hanyoyin samun bayanai(links) da ba a bukata sakamakon bukatar hakan daga Birtania.

A shekarar 2012 ne Hukumar Tarayyar Turai ta wallafa tsare-tsare kan dokar fitar da bayanan.

Inda ta bai wa mutane damar gabatar da bukatarsu ta neman a fitar da bayanai a kansu idan ba sa son zaman bayanan a rumbun kamfanonin samar da bayanai ta intanet.

Sai dai kuma ba komai ne Google yake yarda ya fitar daga rumbunsa ba.

Inda ya bayar da misalin wasu bukatu biyu da yaki amince wa da su.

Ya ce akwai bukatar da wani jami'in gwamnatin Birtania ya gabatar ta son a fitar da hanyar samun bayanan da wata kungiyar dalibai ta yi na neman a cire shi daga mukaminsa.

Google ya kuma ki amince wa da bukatar wani tsohon malamin addinin kirista, da ya bukaci a fitar da hanyoyin samun wasu kasidu a kan binciken zargin lalata a kansa.