Ali Mazrui ya rasu

Image caption Ali Mazrui ya shahara a fannin rubuce-rubucen addinin musulinci da siyasa

Fitaccen marubicin nan dan kasar Kenya, Farfesa Ali Mazrui ya rasu.

Farfesa Mazrui ya rasu ne a Amurka yana da shekaru 81 a duniya.

Farfesa Mazrui ya yi fice wajen rubuce-rubuce musamman a kan siyasar duniya da addinin musulinci.

A shekarun 1980 ya kaddamar da wani shirin talabijin a BBC mai suna The Africans - a Triple Heritage' a turance, wanda ya yi farin jini.