Boko Haram: Za a yi taro a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Boko Haram ya kashe mutane akalla 13,000 daga 2009 inji shugaban Najeriya

A ranar Litinin din nan ne ministocin harkokin waje na Najeriya da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Benin da kuma Nijar za su yi taro domin cimma matsaya kan dokokin da suka dace kan yaki da 'yan Boko Haram a kan iyakokin kasashen.

Mahalatta taron za su tattauna akan wani daftrain doka ne da kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen Afrika ta Au suka amince da shi kan yadda sojojin kasashen za su fuskanci masu tayar da kayar baya.

Taron na wuni guda wanda zai gudana a Abuja babban birnin Nigeria zai kuma samu halartar ministocin tsaro na kasashen biyar da ke makwabtaka a yankin kuma zai kasance karkashin hukumar raya tafkin Chadi da Jamhuriyar Benin.

Za kuma a yi shi ne a matsayin cigaba na wanda aka yi ranar bakwai ga watan Oktoban nan a J amhuriyar Nijar.

Karin bayani