Burtaniya za ta yi muhawara a kan Palasdine

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin wata wasika, kusoshin sun ce sun yi imani wanzuwa da tsaron Isra'ila sun dogara ne a kan kasancewar kasar Palasdinawa

'Yan majalisar dokokin Burtaniya za su tafka wata muhimmiyar muhawara a Litinin din nan a kan ko ya kamata gwamnati ta dauki yankin al'ummar Palasdinawa a matsayin kasa.

Da wuya matakin ya shafi manufofin gwamnatin Burtaniya, amma dai ana sa ran zai daukaka martabar siyasar wannan batu.

Kudurin wanda wani dan jam'iyyar Labour ya gabatar, ya biyo bayan shawarar da Sweden ta yanke a farkon wannan wata ta martaba Palasdine a matsayin kasa, wakiliya ta farko a cikin tarayyar Turai da ta yi hakan.

Daruruwan kusoshi a Isra'ila ne da ke da ra'ayin kawo sauyi ciki har da tsoffin 'yan majalisar Isra'ila Knesset suka bukaci Burtaniya ta bi sahu.