Bishop-Bishop sun amince da 'yan luwadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ce Paparoma Francis na da sassauci kan 'yan luwadi fiye da wanda ya gada.

Wani daftari da limaman cocin katolika su kusan 200 wadanda ke halartar taron sake nazarin darussan da Cocin ke koyarwa don iyalai, ya kalubalanci cocin da ya sassauta matsayinsa akan'yan luwadi

Daftarin ya ce 'yan luwadi da madigo suna da wata baiwa da halaye da za su iya amfanarwa ga al'umma, ba tare da sun sabawa dokokin asali na al'ada ba.

Sakatare na musamman na taron Bishop-Bishop din na katolika Monsignor Bruno Forte , ya ce dole ne Cocin ya mutunta 'yan luwadi da madugo.

Mr Forte ya kara da cewa a wurinsa mutanen da suka zabi wata dabi'a da ake gani ta daban ce su ma suna da dama da 'yanci da ya zama dole a kare musu.

Sai dai ya ce har yanzu akwai cece-kuce da ake yi game da kalaman da aka yi amfani da su a daftarin.