Bring Back Our Girls za ta yi zanga-zanga

Kungiyar Bring Back Our Girls Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Kungiyar Bring Back Our Girls

Yau talata 14 ga watan Oktoba - aka cika watanni 6 cif-cif da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan Makaranta su fiye da dari biyu daga garin Chibok na jihar Borno.

Gwamnatin Nijeriya dai ta yi alwashin cewa sojojinta za su kubutar da 'yan Matan, to amma har yau, watanni 6, suna hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Kungiyoyi dabam-dabam a Nijeriya suna ta gudanar da tarukka na cikar watanni 6n tun lokacinda aka sace 'yan Matan a ranar 14 ga watan Aprilu.

Hadiza Bala Usman tana cikin masu wannan fafutuka a kungiyar "BringbackOurGirls" don ganin an kubutar da 'yan Matan, ta bayyana cewar a yau za su yi tattaki zuwa Fadar gwamnatin Nijeriya don kai koke da tambayar me yasa har yanzu ba a kubutar da 'yan Matan ba.

Karin bayani