Ebola ta hallaka ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya

Image caption Cutar dai ta fi tsamari a kasashen Afirka ta yamma uku, Liberiya da Saliyo da kuma Guinea

Wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya da ake yi wa maganin cutar Ebola a kasar Jamus ya mutu.

A cikin makon jiya ne aka dauko jami'in dan kasar Sudan wanda ba a bayyana sunansa ba daga kasar Liberia zuwa birnin Leipzig don yi masa magani a wani asibiti na musammam.

Jami'an asibitin sun ce an killace shi a wani daki inda aka dinga ba shi maganin gwaji na cutar Ebola.

Jami'in na daya daga cikin mutane uku da ake yi wa maganin cutar Ebola a Jamus.

Rahotanni sun ce daya daga cikin mutanen uku yana samun sauki.

A wani al'amarin daban kuma, Burtaniya ta fara tantance fasinjoji yau a filin jirgin saman Heathrow da ke London.

Za a yi tambayoyi ga mutanen da ke shiga Burtaniya daga kasashen Afirka ta yamma wadanda cutar ta fi addaba, Liberiya, Saliyo da Guinea, kuma a gwada yanayin zafin jikinsu.