WHO ta ce dubban mutane na iya kamuwa da Ebola a mako

Ma'aikatan kiwon lafiya Hakkin mallakar hoto GETTY
Image caption Ma'aikatan kiwon lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa adadin wadanda ke harbuwa da cutar Ebola a shiyyar Afirka ta yamma zai iya kaiwa dubu goma, nan da karshen shekara.

Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Lafiya ta Duniyar, Bruce Aylward ya bayyana cewa kusan kashi saba'in bisa dari na wadanda ke kamuwa da cutar na cikin mummunan yanayi.

Hukumar lafiyan ta kuma yi gargadin cewa, adadin mutanen da ke kamuwa da cutar ta Ebola a yammacin Afrika zai iya kaiwa dubu biyar zuwa dubu a kowanne mako nan da karshen shekarar nan.

Kawo yanzu dai kimanin mutum 4500 ne cutar Ebolar ta halaka.