Mutane kusan 4500 ne suka mutu sanadiyar ebola - WHO

Image caption Hukumar ta yi kira ga kasashen duniya su tallafa a shawo kan cutar

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce ya zuwa yanzu mutane 4,447 suka mutu sakamakon kamuwa da kwayar cutar ebola.

Hukumar ta kara da cewa tana sa rai adadin mutanen da za su kamu da cutar ya zarta dubu tara ya zuwa karshen makon da muke ciki.

Mataimakin Babban daraktan hukumar, Bruce Aylward, ya ce akasarin mutanen da suka kamu da cutar suna zaune ne a yankuna 19 a kasashen Sierra Leone da Liberia da Guinea, yana mai cewa cutar na ci gaba da yaduwa a wasu yankunan.

Dr Aylward ya nuna matukar damuwa kasancewa cutar na yaduwa a manyan birane da kuma wasu yankuna da ke kan iyaka da kasar Cote d'Ivoire.

Ya yi kira ga manyan kasashen duniya su bayar da tallafin kudi da na jami'an kiwon lafiya domin a yi amfani da su a kasashen da cutar ta yi kamari.

Karin bayani