IMF ta zargi Nijar da saba wa sharuda

Shugaba Muhammane Issofou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammane Issofou

A Jamhuriyar Nijar, Asusun ba da lamuni na duniya, IMF ya zargi gwamnatin kasar da gudanar da wasu harkokin kudi ba bisa ka'ida ba.

Hasali ma, asusun ya koka da cewa gwamnatin ta Nijar ba ta shawartar sa kafin zartar da wasu ayyuka sabanin yarjejeniyar da suka amince da ita na yin haka.

Asusun ba da lamunin na duniya ya bayyana wannan matsayin nasa ne a cikin wani rahoto da ya wallafa sakamakon wata ziyarar aiki da ya kai Nijar a cikin watan Satumban da ya gabata.

Tuni dai 'yan adawa na Nijar suka nuna gamsuwarsu da matsayin Asusun, suna masu cewa rahoton ya gaskata zarge-zargen da suka yi wa gwamnatin a baya cewa tana saba ka'ida.

Karin bayani