Isra'ila ta soki lamirin kuri'ar Burtaniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya na ziyara a zirin Gaza, inda yake tattaunawa da jami'an Palasdinawa

Isra'ila ta soki lamirin wata kuri'a da majalisar dokokin Burtaniya ta kada da ke bukatar gwamnati ta martaba yankin al'ummar Palasdinu a matsayin kasa mai 'yancin cin gashin kai.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta fitar ta ce kuri'ar za ta yi nakasu ga yunkurin samun nasarar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kuma aika abin da ta kira wani sakon tada husuma ga shugabanci Palasdinu.

Ministocin gwamnatin Burtaniya dai sun kauracewa zaman kada kuri'ar kuma ba lallai ne matakin ya yi tasiri a kan manufofin kasar ga Palasdinawa ba.

Sai dai, jakadan Burtaniya a Isra'ila ya bayyana cewa kuri'a ta bayyana ra'ayin al'ummar Burtaniya ne.