An kori 'yan sanda daga aiki saboda ''sumbata''

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rundunar 'yan sandan kasar ta ce halayyar da suka yi a bainar jama'a ba ta da kyau

A kasar Tanzania, an kori wasu 'yan sanda daga aiki bayan da wani hoto da ya nuna su suna sumbatar juna.

'Yan sandan guda biyu -- mace da namiji - na yin aiki ne a matsayin 'yan sandan kan hanya, sai kawai suka fara sumbatar juna suna sanye da kayan aiki.

Dan sanda na uku da ke tare da su ne ya dauki hotonsu, kana ya sanya shi a shafin intanet, lamarin da ya ja hankalin 'yan kasar har ta kai suna bayyana mamakinsu a shafukan sada zumunta da muhawara.

Wannan al'amari dai ya faru ne a garin Kagera da ke arewa maso yammacin Tanzania.

Kwamandan 'yan sandan yankin, Henry Mwaibambe, ya shaida wa BBC cewa an kori 'yan sandan daga aiki ne saboda halayar da suka yi ba ta da kyau, musamman ganin cewa sun yi hakan ne a bainar jama'a.

Sai dai wasu 'yan kasar sun ce matakin da aka dauka a kan 'yan sandan ya yi tsauri.

Daya daga cikinsu ya wallafa a shafin Facebook dinsa cewa: "na taba ganin hoton tsohon shugaban Amurka marigayi Reagan yana sumbatar matarsa a fadar shugaban kasa kuma babu wanda ya ce a tsige shi saboda hakan", don haka bai kamata a kore su ba.

Karin bayani