An yi artabu da 'yan Boko haram a Kamaru

Shekau Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Shekau

Wasu bayanai na tabbatar da cewa a daren yau, Laraba, an yi ta musayar wuta tsakanin 'yan Boko Haram da dakarun kai daukin gaggawa na Kamaru, a garin Amchide mai iyaka da Banki na Najeriya.

Sai dai babu wani bayanai dake nuna ko an samu asarar rayuka, ya zuwa yanzu.

Sai dai a sakamakon wannan tashin hankalin, jama'a da dama da BBC ta tuntuba ta waya, sun ce sun tsere daga garin sun shiga daji.

Wanna dai ba shi ne karon farko da mayakan kungiyar suka kai farmaki a garin na Amchide ba.