Hatsarin jirgi ya janyo mutuwar 'yan mata 10

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rashin kiyaye ka'idojin sufurin jiragen ruwa na daga cikin abubuwan da ke haddasa irin wadannan hadurra

Wasu 'yan mata 10 sun mutu, yayin da ake ci gaba da neman karin wasu biyu, bayan wani kwale-kwale ya kife da su a cikin kogi a garin Lanjan na karamar hukumar Garun Malam da ke jihar Kano a Nigeria.

Wani darakta a hukumar ba da agajin gaggawa ta Kano SEMA Abdullahi Aminu, ya shaida wa BBC cewa matukin jirgin ne kawai ya tsira a lokacin da kwale-kwalen ya kife da su.

Jami'in ya ce jami'ian hukumar sun je yankin domin ba da dukkan taimakon da ya kamata, saboda har yanzu akwai mutane biyu da ba a gano ba a cikin kogin.

Rahotanni sun ce hatsarin ya auku ne sakamakon ruwan sama da ya haddasa cikowar kogi.

Rahotanni sun ce matukin jirgin ya yi ninkaya inda ya tserar da kansa, amma bai iya kubutar da 'yan matan ba a wannan kogi da ke toroko.

Hatsarin jiragen ruwa a Nigeria na yawan faruwa kuma akasari ana danganta hakan ne da dora musu fasinja da kaya fiye da kima da raunin harkar kula da gyaran jirage da kuma rashin ingantattun fitilu.