Fadada sakonni ta waya game da Ebola

Masu fama da cutar Ebola Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu fama da cutar Ebola

Masu kula da tsarin aikewa da sakonni ta wayar salula dake gargadi game da cutar Ebola a Saliyo sun ayyana fadada tsarin ya kai sauran wasu kasashe 7 na Yammacin Afrika.

Tsarin dai ya baiwa kungiyoyin bayar da agaji da Red Cross da Red Crescent damar aikewa da sakonni ta wayoyin salula ga kowacce waya a wasu yankuna na musamman ta hanyar zanen yanayinta a wata zayyana ta musamman na'urar Komputa.

Haka kuma ba tare da wani bata lokaci ba, tsarin yana maida amsar kowanne sako da aka turo ta wannan hanyar.

Kungiyoyin agajin sun ce suna fatar kammala aikin fadada tsarin cikin watanni 9 masu zuwa.

Sai dai kuma za su bukaci hadin kai na kamfanonin sadarwa ta wayar salula da hukumo na wadannan yankuna.

Robin Burton na gamayyar kungiyoyin agaji na Red Cross da Red Crescent ya ce, "Wannan tsari yana yin tasiri matuka a kasar Saliyo inda ake aikewa da sakonnin ta wayar salula kimanin miliyan 2 a kowanne wata, wanda ke taimakon al'ummomin a yankin su kula da kariyar lafiyar su, su guji kamuwa da cutar, idan kuma suka kamu da ita, su san matakan da za su dauka."

Ba kamar Talabijin ba, ya ce, "idan muka aike musu da sakonni ta waya, sakonnin suna nan ajiye a caikin wayar su".

Kasashen 7 da aka shirya gwada wannan tsari da ake kira TERA System, sun hada da Benin da Togo da Ghana da Mali da Guinea Bissau da Gambida da Burkina Faso.

An fara amfani da wannan tsari ne na TERA a kasar Haiti sakamakon girgizar kasar da yi mummunar barna a kasar a shekara ta 2010.

Daga bisani aka kai shi kasar Saliyo a shekara ta 2013 bayan kamfanin waya na Airtel shiyyar kasar ya amice ya kafa na'urar da ta wajaba don tsari irin wannan a lokacinda mummunar annobar Kolera ta barke a kasar wadda ba taba ganin irin ta ba tun kimanin shekaru 40 da suka gabata.

Karin bayani