'Kokarin duniya a kan Ebola bai isa ba'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fiye da mutane dubu hudu ne suka mutu sakamakon cutar Ebola ya zuwa yanzu

Shugaban Amurka, Barak Obama ya ce kokarin da duniya gaba daya take yi don shawo kan cutar Ebola, bai wadatar ba.

Nan gaba a Larabar nan ne, Barak Obama zai gudanar da tattaunawa ta bidiyo da shugabannin Burtaniya, Faransa da Jamus da kuma Italiya kan wannan batu.

Tun da farko, shugaban jami'an yaki da cutar Ebola na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci duniya ta dauki mataki cikin hanzari, inda ya yi gargadin cewa babban abokin gaba a yunkurin magance Ebola shi ne lokaci.

Anthony Banbury ya yi gargadin cewa duk da kokarin shawo kan Ebola da ake yi, amma cutar na kara samun galaba.

Don haka ya yi kira a samar da karin kudade don gina cibiyoyin lafiya a Saliyo, Guinea da Liberiya da kuma samar da karin ma'aikatan lafiya da za su kula da majinyata.