Cutar Ebola ta sa an killace minista

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana fargabar cewa cutar za ta kara muni matukar kasashen duniya ba su himmatu wajen yaki da ita ba.

An killace Ministar sufurin kasar Liberiya, Angela Bush bayan mutuwar direbanta sakamakon cutar Ebola.

Ministar ta fada wa BBC cewa ta karbi wani rubutaccen sakon waya daga direban nata a karshen mako da ke shaida mata cewa ba shi da lafiya.

Jim kadan da faruwar wannan al'amari kuma sai aka shaida mata cewa ya mutu a wannan kasa da cutar Ebola ta fi muni.

Fiye da rabi na kimanin mutane dubu hudu da dari biyar da suka mutu sakamakon cutar Ebola sun mutu ne a kasar Liberiya.