Ministoci bakwai sun yi murabus a Nigeria

Image caption Tun tuni ake sa ran ministocin za su bar aiki saboda burinsu na tsayawa takara a jihohinsu

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya sanar da cewa ministocinsa guda bakwai sun ajiye mukamansu a yau.

Shugaban wanda ya sanar da hakan yayin taron mako-mako na majalisar zartarwar kasar da ake yi kowacce Laraba, ya ce ministocin sun nuna sha'awa ne na shiga zabukan shekarar 2015.

Wadanda suka yi murabus din sun hadar da ministan yada labarai, Mr. Labaran Maku da na ciniki da masana'antu, Samuel Ortom da karamin ministan ilmi, Nyesom Wike da kuma karamin ministan tsaro, Musiliu Obanikoro.

Sauran su ne ministan kwadago, Emeka Wogu da Farfesa Onyebuchi Chukwu, ministan lafiya sai karamin ministan Neja Delta, Darius Ishaku.

Ministocin wadanda tun tuni ake sa ran barin aikinsu, za su tsaya takara a zabukan gwamnonin jihohinsu ne.