Ranar Matan Karkara ta duniya

Matan karkara na Nijer Hakkin mallakar hoto Mike Goldwater World Vision
Image caption Matan karkara na Nijer

Laraba 15 ga watan Oktoba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe don Matan Karkara a duniya.

Wannan rana tana la'akari da muhimmiyar rawa da gudunmuwar da Matan karkara ke bayarwa wajen bunkasa noma da raya karkara da wadata duniya abinci da kuma kawar da fatara.

Matan dai na taimakawa a wajen ayyukan gona da sauran sana'o'i don kyautata rayuwar Iyali. Sai dai kuma akasari suna rayuwa ne cikin mawuyacin hali.

Yawancin Matan karkara kamar a Nijer misali, sun yi koken cewa tallafin da suke samu bai taka kara-ya-karya ba daga gwamnati.

Karin bayani