Badeh: Kamaru na ba mu hadin kai amma...

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A baya Nigeria ta zargi Kamaru da rashin bata hadin kai wajen yakar Boko Haram

A Nigeria, ranar Jumu'a ne manyan hafsoshin tsaron kasar da na Kamaru ke kammala ganawa ta kwanaki uku da suke yi tsakanin su.

Manufar ganawar ita ce samar da wani dandamali guda, inda dakarun tsaron kasashen biyu zasu hada hannu wajen yakar ayyukan tayarda kayar baya.

A baya dai Najeriya ta yi korafin cewa Kamaru bata bada hadin kan daya kamata a yakin da ake yi da 'yan kungiyar Boko Haram.

Sai dai babban hafsan tsaro na Nigeriar, Air Marshal Alex Badeh ya ce 'ai ba wai ba sa ba da goyan baya ba ne, suna ba da goyan baya amma yadda suke so suke yi'.

Air Marshal Alex Badeh ya kara da cewa 'amma yanzu zamu zauna tare mu ga yadda za mu yi aiki babu wata tangarda'.