An ce Boko Haram na nufa Chadi

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Abubakar Shekau

Rahotani na cewa hukumomi a kasar Chadi na tsaurara matakan tsaro, sakamakon wasu rahotannin dake cewa ana ganin wasu 'yan bindiga da suke nufa kasar daga wasu yankuna na Nijeriya da Kamaru.

Rahotannin na cewa mutanen, wadanda ake zargin yan Boko Haram ne, na ratsawa ne ta garin Darak mai makwabtaka da tafkin Chadi a lardin arewa mai nisa.

Wasu na zargin cewa artabun da ake yi da su ne ke tilasta masu tserewa.

Mazauna yankin na cewa ana tsaurara bincike, kuma jama'a yanzu haka na fargabar fita da dare.