BBC ta kaddamar da yaki da ebola a WhatsApp

Image caption BBC ta ce matakin zai rage masu kamuwa da cutar ebola

BBC ta kaddamar da wani shiri na wayar da kan jama'a game da cutar ebola a manhajar shafin sada zumunta na WhatsApp.

BBC ta yi hakan ne domin amfanin masu hulda ta ita a yankin yamacin Africa inda cutar ta yi kamari.

Manahajar za ta rika fitar da sakonni da dumi-duminsu wadanda ake sauraro da karantawa da kuma hotuna a kan yadda za a magance cutar.

Za a rika bayar da sakonnin ne a harsunan Turancin Ingilishi da Faransanci.

Idan ka/ki na son shiga wanna shafi na WhatsApp, sai ku aika 'JOIN' zuwa wannan lambar: +44 7702 348 651.

Idan kuma kuna so ku fita daga cikin manhajar sai ku aika da 'STOP' ta hanyar WhatsApp zuwa +44 7702 348 651.

Karin bayani