An kai kayan agajin farko kan ebola daga Ghana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jirgin saman ya dauki kayan agajin ne zuwa kasashen da ebola ta fi shafa

A birnin Accra na kasar Ghana, ranar Alhamis ne jirgin saman farko dauke da kayan agaji zuwa kasashen da cutar ebola ta shafa ya tashi daga filin jiragen saman zuwa kasashen.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ayyana Ghana a matsayin zangon girke kayan agaji da magunguna da kuma jami'an kiwon lafiya kafin daga bisani a tura su zuwa kasashen.

Shugaban kasar ta Ghana, John Mahama, shi ya ba Majalisan Dinkin Duniyar damar amfani da kasar wajen jigilar kayan agajin.

A kasashen Liberia da Sierra Leone da Guinea ne dai cutar ta fi kamari.

Karin bayani