'Amurka da Turai ba sa fuskantar mummunar ebola'

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption WHO ta ce Amurka da Turai suna da tsarin kiwon lafiya mai karfi

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce tana da yakinin cewa zai yi matukar wuya a samu mummunar barkewar annobar cutar Ebola a Amurka ta arewa da kuma a yammacin Turai, inda ake da tsarin kiwon lafiya mai karfin gaske.

Wani babban jami'in hukumar ya ce duk da kasancewa bullar cutar a yammacin duniya babban abin damuwa ne, amma kasashen za su iya daukar matakan kariya.

Faransa ta bayyana cewar zata soma bincike a kan fasinjojin da ke isa kasar daga Guinea, daya daga cikin kasashen da cutar ta Ebola ta shafa ainun.

Ranar Alhamis ne dai ministocin lafiya na kasashen tarayyar Turai ke wani taro domin tattaunawa kan matsalar.

Karin bayani