An sallami dan- autan Joe Biden daga aikin soja

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan autan Joe Biden ya yi nadama

An sallami dan- autan mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden daga aikin soja, bayan gwajin da akai masa ya nuna cewa yana zukar hodar ibilis.

Gwajin amfani da kwayoyin da aka yiwa Hunder Biden- sojan ruwa- a watan Yunin bara, ya gano cewa yana shan hodar ibilis, kuma an kore shine a watan Fabrariru

Mr Biden mai shekaru 44 yace ya yi nadamar wannan al'amari, kuma yace yaji kunyar cewa abinda yake aikawata yayi sanadiyyar korarsa daga aiki.

A wata sanarwa daya fitar, yace yana mutunta hukuncin da rundunar sojin ruwan ta yanke masa