An yi suka ga 'yan majalisa saboda kudin fansho

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan majalisar wakilan sun amince a bai wa shugabannin majalisar dokoki kudin fansho har karshen rayuwarsu

Masu fafutuka a Nigeria sun fara mayar da martani kan wata doka da 'yan majalisar wakilan kasar suka amince da ita, ta bai wa shugabanin majalisun dokokin kasar kudaden fansho har karshen rayuwarsu.

Ranar Laraba ne 'yan majalisar wakilan suka amince da wannan mataki na biyan kudaden fansho na har karshen rayuwa ga shugabannin majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai da mataimakansu wadanda suka kammala wa'adinsu ba tare da an tsige su ba.

Sai dai Alhaji Abdulkarim Dayyabu, shugaban Rundunar Adalci, mai rajin kare hakin jama'a, ya ce shugabanin majalisun ba su cancanci wannan karramawar ba.

Ya kara da cewa hakan son kai ne, musamman ganin cewa 'yan kasar na fama da matsanancin talauci.

Karin bayani