An kori dan Joe Biden daga aikin soja

Joe Biden Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden

An sallami dan-autan mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, daga aikin soja bayan gwajin da akai masa ya nuna cewa yana shan hodar ibilis.

Gwajin amfani da kwayoyin da aka yi wa Hunder Biden - sojan ruwa- a watan Yunin bara ya gano cewa yana shan hodar ibilis, kuma an kore shi ne a watan Fabrairu.

Mista Biden, mai shekaru 44, ya ce ya yi nadamar wannan al'amari, yana mai cewa ya ji kunyar cewa abin da ya aikata ya yi sanadiyyar korarsa daga aiki.

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce yana mutunta hukuncin da rundunar sojin ruwan ta yanke masa.