Ebola: Nabarro ya kare yunkurin kasashen duniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar MSF ta ce taimakon da kasashen duniya suke bayarwa kan cutar ebola baya tasiri sosai

Jami'in Majalisar dinkin duniya akan cutar Ebola David Nabarro ya kare kokarin da kasashen duniya suke yi na dakile barkewar cutar a Yammacin Afirka.

Jami'in na maida martani ne ga sukar da kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta yi, na cewa alkawuran da kasashen duniya suka yi na kai agaji zuwa yankin bai yi tasiri ba tukuna akan annobar.

Mr, Nabaro ya fadawa BBC cewa shirye shirye sun yi nisa wajen samarda gadajen marasa lafiya guda 4,000 zuwa wata mai zuwa, idan aka kwatanta da guda dubu- ukun da aka samar a karshen watan Agusta.

Ebola ta kashe mutane fiye da 4,000 yanzu haka