Nigeria da Boko Haram sun tsagaita wuta

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Babban Hafsan Tsaron Nigeria, Alex Badeh, ya ce dukkan dakarun kasar za su dakatar da bude wuta

Gwamnatin Nigeria ta bayar da sanarwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Boko Haram.

Babban Hafsan Tsaron Nigeria Air Chief Marshal Alex Badeh ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a karshen wani taron hadin gwiwa da suka yi da manyan hafsoshin soji na Kamaru.

Sai dai bai yi karin bayani game da sharuddan tsagaita bude wutar ba.

Shi ma wani mataimaki na musamman ga Shugaba Goodluck Jonathan, Hassan Tukur, ya tabbatar da labarin.

Ba wannan ne karo na farko da ake bayar da sanarwa irin wannan ba, amma daga bisani 'yan kungiyar Boko Haram su musanta.

Har yanzu dai babu wani martani daga kungiyar Boko Haram game da wannan batun.

Karin bayani