Seyni Omar: Gwamnatin Nijar ta maida martani

Shugaba Mahamadu Isufu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Mahamadu Isuf

Gwamntain Nijar ta maida martani kan zargin da jagoran 'yan adawar kasar Alhaji Seyni Omar ya yi wa shugaba Mahamadu Isufu.

Jagoran 'yan adawan ya zargi shugaban kasar da fallasa jam'iyun siyasa na bangaren adawa tare da yi wa shugabbanninsu bita da kulli.

Sannan ya koka har ila yau game da mumunar ta'asar da gwamnatin kasar ke tafkawa dangane da yadda take sarrafa kudin kasa, musaman jirgin shugaban kasa da ya ce kudinsa ya wuce kima.

Sai dai Ministan harkokin wajen kasar , kuma shugaban jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki malam Bazoum Mohamed, ya ce ko kadan zargin na Seyni Omar ba shi da tushe.