Cuwa-cuwar makamashi a Spain

Image caption Masu bincike ne suka gano mitocin nada matsala

Masu bincike sun gano cewa za'a iya yiwa mitocin wuta da ake amfani da su a wurare daban daban a Spain kutse domin rage yawan makamashin da ake amfani da shi

Mahara ka iya yin kutse cikin na'urorin saboda wasu abubuwa marasa inganci da ke cikinsu kamar yadda masu binciken suka yi gargadi

Sai dai kamfanin da ya samar da mitocin yanzu na aikin inganta tsaron na'urorin

Wannan abu da aka gano na zuwa ne yayinda wani kwararre kan harkar tsaro ya yi gargadin cewa kungiyoyin 'yan ta'adda ka iya kai hari ga hanyoyin ababan more rayuwa da suke cikin yanayi mara kyau

Hakkin mallakar hoto AP

Kamfanonin wuta da dama na makala irin wadannan mitoci domin taimakawa kwastomomi wajen iya gane yawan wutar da suke amfani da ita da kuma taimaka musu wajen iya tattalin makamashinsu ta hanyar data kamata

Wani mai gudanar da bincike mai zaman kansa Javier Vidal ya ce 'mun debi wasu domin ganin yadda za su yi aiki inda kuma muka gano raunin dake tattare da su

'Mun yi zargin cewa za'a iya samun wasu abubuwa marasa kyau tare da mitocin abinda ya sa muke son mu bincika'

Ya fadawa BBC cewa ' mun ji tsoron za'a iya yi musu kutse cikin sauki kuma mun tabbatar da hakan'